Courtois ya tsare ragar Real Madrid karo na 200 – BBC

wp header logo 196.png

Asalin hoton, Real Madrid FC
Ranar Lahadi Thibaut Courtois ya tsare ragar Real Madrid karo na 200 a wasan Spanish Super Cup a birnin Riyadh, Saudi Arabia.
To sai dai Barcelona ce ta yi nasara a kan Real Madrid da ci 3-1 ta kuma dauki kofin karo na 14, bayan da Real ce ke rike da shi na bara na 12 jumulla.
Mai tsaron ragar ya yi wadan nan wasa a kaka biyar da yake taka leda a Santiago Bernabeu, inda ya samu damar lashe kofi bakwai a kungiyar.
Cikin kofunan har da Champions League da Club World Cup da European Super Cup biyu da Spanish Super Cups biyu.
Golan wanda ya lashe kyautar kofin Yashin, ya taka rawar gani a wasannin Real Madrid a 2022 har da daukar Champions League a kakar.
A wasan da Real Madrid ta ci Liverpool a Faransa ta lashe Champions League, Courtois ne aka zaba wanda ya fi taka rawar gani a fafatawar.
Mai taston ragar tawagar Belgium ya yiwa Real wasa 200 a gasa shida, inda ya tsare raga sau 147 a La Liga da 41 a Champions League da bakwai a Spanish Super Cup da biyu a Copa del Rey da biyu a Club World Cup da daya a Uefa Super Cup.
 
© 2023 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *